Thursday, December 4, 2025

Pharmacist Ahmed Ibrahim Yakasai murnar ƙarin shekara guda mai albarka a cikin rayuwarsa.

PHARMACIST AHMED IBRAHIM YAKASAI
:-Jagora Mai Gina Al’umma ya chika shekaru 65

Daga Kabir Saidu Danladi Funtua

A cikin duniyar da ake buƙatar shugabanni masu hangen nesa, ɗabi’a, da kishin mutane, akwai wasu mutane da fitilarsu ba ta gushewa. A Najeriya musamman a fannin kiwon lafiya, irin wannan haske ya bayyana ta fuskar Pharmacist Ahmed Ibrahim Yakasai — Wanda taimako da tallafinsa sun haɗa fannoni da yawa tun daga ilimi, jagoranci, alheri, kasuwanci, da bauta wa al’umma. 

An haife shi a 1 Ga watan Disamba, 1960, kuma tun Yana dan karami ya fara karatun Allo, Islamiyya da karatun zamani. daga wannan lokacin ya fara tafiyar da ta zamo ginshiƙi ga dubban mutane.
Tafiya sannu sannu kwana nesa, a shekarar 1983
 Pharm. Yakasai ya nuna cewa ilimi  tafiya ce wacce ake ci gaba da bin ta, babu tsanyawa, domin ya yi karatu zamani tun daga matakin Primary har Jami a. Ya gama karatun Degree na farko a Jami ar Ahmadu Bello da ke Zaria wanda ya gama a shekarau 1983.

Daga nan kuma ya yi ta yin karatu da nazarin kwasa kwasai  a sassa daban-daban na fading duniyar nan, yin hakan ya bashi hikima da fasaha Kala Kala wanda sukayi tasiri a rayuwar sa. 

Alhaji Ahmed Ibrahim Yakasai ya yi karatu mai zurfi a University of Salford, Manchester (UK)  Inda ya Karanchi fasahar  zamani. 

A wannan zamanin na yanzu kasar Sin: China  ita che makura ilmin zamani, Alhaji Ahmed  ya yi karatu a Fudan University (China)  Inda ya Karachi  jagoranci da tsare-tsare

Ya kuma yi karatu a University of South Africa in da ya yi karatun  gudanarwa da cigaba


Wannan karanche karanchen sune suka  gina masa irin ƙwarewarsa da ta sa ya  zama tubalin ginin Al umman. 


 MATAKIN JAGORANCI 

A matsayinsa na ƙwararren masanin magunguna, bai daɗe da gama karatun Jami a  ba sai da ya zama gwani kwararre mai tasiri a tsakanin jami’an lafiya. Ya rike manyan mukamai kamar:

Shugaban Pharmaceutical Society of Nigeria (2015–2018)

1st Deputy President, PSN (1997–2000)

Chairman PSN Kano (1991–1995)


Lokacin da ya jagoranci PSN, ya yi suna wajen kawo haɗin kan dukkan ƙwararru cikin kiwon lafiya, da kuma yaƙi da magungunan jabu da ya zama babbar barazana a ƙasar nan.


A Dukkan ayyukan da yayi  a Ko Ina sai da ya bar tarihin aiki da rayuwa abin koyi. 

Pharmacist Yakasai bai tsaya ga fannin Pharmacy kaɗai ba. Gwamnatin Kano ta gane ƙudurin sa na gaskiya, son cigaban Al umman da tallafa wa rayuwarsu, saboda haka ta ba shi manyan mukamai biyu masu muhimmanci Kamar haka:

Kwamishinan Ma’adanai, Kasuwanci da Yawon Shakatawa (2005–2010) da kuma

Kwamishinan Ƙasa da Tsare-Tsaren Birane (2010–2011)


A karkashin sa an ƙarfafa masana’antu, an jawo jari, kuma an yi tsare tsaren birane cikin natsuwa da hangen nesa wanda hakan ya kawo chi gaba mai yawa a man aikatar. 


 GININ MASANA’ANTU 

A 1992, ya kafa Pharmaplus Nigeria Ltd, Kamfani da ya   zamo ɗaya daga cikin manyan gidajen magunguna da kuma cibiyar bada shawara ga NAFDAC da sauran hukumomi.

Haka kuma yana da kamfanonin:

Multiplus CONSULTING da kuma

Multiplus Resources Ltd


Ƙwarewar sa ta sanin yadda ake jujjuya da tsara kamfanoni  ta sa ya taimaka wajen shigo da kayayyakin kiwon lafiya da dama cikin Kasar nan bisa kula da tsari.

MALAMI, MASANI , MAI GINA MATASA 

Ko da yake ya yi fice a gwamnati da kasuwanci, duk da hakan Bai yardar tallafawa MATASA ba a dukkan matakan rayuwar sa. A wannan fannin ya taimaka wa MATASA Wajen samun aiyuka da shiga jami'o'in Najeriya. 

A matsayinsa na malami a ABU Zaria, da wasu jamioin kasar nan da kasar wajen ya taimakawa  jami'o'i da sababbin fasahohi wajen tabbatar da cewa sabon tsarin karatu na pharmacist na Najeriya ya fara a kan ingantaccen tushe.

Matasa da dama suna kiran sa mentor, wasu kuma madubi, wasu har shugaban da ya fi kusa da mutane.


GININ AL’UMMA DA KUNGIYOYI 

Alherinsa ya kai shi kafa Safe Medicines Foundation, wacce ke yakin magungunan jabu da tallafawa jama’a da bincike.

Haka kuma yana cikin manyan kungiyoyin duniya, ciki har da:

Society for Family Health (SFH) da kuma NAPPSA


Ayyukan sa a cikin gida da waje sun yi tasiri mai zurfi wajen kare lafiyar jama’a.

KARRAMAWA DA SARAUTA 

Al’umma ta yabi nagartarsa da kwazonsa. An bashi muqamai, lambobin yabo da darajoji da dama, ciki har da:

Fellow PSN, 

Fellow Nigeria Academy of Pharmacy da

Fellow Institute of Logistics Management. 

SARAUTA KACHALLAN KANO

A shekarar 2023, an ba shi sarauta mai ɗimbin tarihi ta Kachallan Kano, alamar jarumtaka, hikima da hidima ga jama’a.

Masautar Kano ta Amina da halayyarsa da dimbin gudunmawarsa Ga Al umman gaba daya kafin ta Amina da nada mashi sarautar KACHALLAN KANO a fadar Mai Martaba Sarkin Kano. 

Duk da tsawon shekaru yana aiki, har yanzu Pharm. Ahmed Ibrahim Yakasai shi ne a kan gaba wajen:-Tunani mai kyau, neman sabuwar dabara,
kare lafiya da nagarta a cikin al'umma.

Rayuwarsa tana koyar da cewa jagoranci ba mukami ba ne — aikin hidima ga Jama'a ne.

A wannan watan Disamba, muna taya Pharmacist Ahmed Ibrahim Yakasai murnar ƙarin shekara guda mai albarka a cikin rayuwarsa.

Allah Ya kara masa lafiya, hikima, nutsuwa, da armashi a dukkan al’amuransa. Allah Ya sanya taimakon da yake yi wa al’umma ya ci gaba da zama haske mai ɗorewa.

Daga Kabir Saidu Danladi Funtua, Blueprint Newspapers, Kano Zonal Office